AUWAL DANLADISakataren kula da tafiyar da jam’iyyar PDP a yankin Neja ta arewa, Mal. Danladi Adamu Tambaya.

 

Daga Awwal Umar Kontagora

Sakataren kula da tafiyar da jam’iyyar PDP a yankin Neja ta arewa, Mal. Danladi Adamu Tambaya (Y’DAT) ya nemi jama’a da su baiwa ‘yan takarkaransu na jam’iyyar PDP daga kasa har sama a zabubbukan kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Sakataren ya bayyana hakan ne a garin Kwantagora lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da zaben shugabancin kananan hukumomi da kansuloli da za a gudanar a ranar Asabar 30 ga watan Disamba, 2019.

Ya ce Jam’iyyar PDP ta shirya tsaf domin lashe zabubbukan kujerun shugabancin kananan hukumomi da kansulolinsu a yankin karamar hukumar mulki ta Kwantagora, dangane da hakan ne ma suka bi ka’idoji da dokokin yakin neman zabe kamar dai yadda hukumar zabe ta jiha ta tsara, “ba mu fargabar komai kuma da yardar Allah muna tare da nasara” In ji sakataren.

Mal. Danladi ya kara da cewar ya zama wajibi duk wani mai kishin jihar nan da ya tabbatar ya sanya ido domin kauce wa magudin zabe, babban aikin da kowa zai yi shi ne amfani da kuri’arsa wajen jefawa ‘yan takarkarun PDP.

Amma maganar tashin hankali ko zagi da sukar abokan takara na wasu jam’iyyu ba mu amince da shi a lokacin yakin neman zabe ba, a sabili da hakan ne aka bukaci matasa da kar su yarda da bangar siyasa ko tashin hankali a lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin da ake zaben. Kowane matashi ya tabbatar ya mallaki katin zabe domin ya sami jefa kuri’arsa a ranar zaben.

PDP dai ta yaba wa jami’an tsaro kan yadda suke gudanar da aikinsu ba tare da tsangwama ko nuna bangaranci ba, don haka ne ma ake kyautata zaton a shirin da gwamnatin jiha ta tanada za a yi adalci ba tare da murdiya ba.

 

TAURARUWA