Daga Garba Bello

buhari1

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Jam’iyyar Adawa ta PDP ta yaba wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa gagarumin nasarar da ya samu wajen kakkabe ‘yan Boko Haram daga Arewa maso gabas, musamman daga mabuyarsu na dajin Sambisa.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP, Prince Dayo Adoyeye, inda ya ce nasarar da aka samu a yakin da ake yi da Boko Haram, ya samo tushe ne daga irin kokarin da gwamnatin baya ta gabatar a shekarar da ta gabata.
Jam’iyyar ta ce, ta jinjina wa Buhari saboda tsayuwar-dakan da ya yi a yakin da aka gwabza tsakanin ‘yan Boko Haram da sojojin Nijeriya bisa jajircewa da kwazon da suka nuna a yinkurin raba kasar nan da ‘yan ta’adda da masu tada kayar baya ke yi a Nijeriya.
A wata sabuwa kuma, tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari inda ya nuna cewar shugaban ya kunyata al’ummar Nijeriya bisa yadda ya gaza wajen cika mafi yawan alkawurran da ya dauka a lokaci yakin neman zabe.
Malam ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe, inda ya bayyana cewa kuskure ne yadda shugaba Buhari ke ci gaba da jefa jama’a cikin halin kuncin rayuwa yau watanni goma sha tara (19) da shugaban ya yi bisa kan karagar mulki babu wani abin-a-zo-a-gani da ya aikata.

TAURARUWA