By Abubakar Hassan

Civil Defence-Corps (NSCDC)

Hakumar tsaro ta “Civil Defence” reshen Jihar Neja ta gano wani kamfanin sarrafa takin zamani na jabu da ke sayar ma manoman jihar da takin.

Kamfanin dai wani gini ne da ke bayan garejin Abdulsalam Abubakar, daura da Otal din Marhaban da ke unguwar Tunga. Majiyar mu ta tsegunta mana cewar hukumar sun sa ma gidan sarrafa takin ido suna ta lura da abubuwan da ke gudana a cikin sa har na kusan tsawon wata daya.

A bisa bayanan da aka samu, an gano cewa masu yin wannan sana’ar suna hada kasa ne da wasu sinadarai  da kuma takin zamani na NPK don sarrafa takin na jabu da suke sazar wa jama’a.

A sa’ilin da wakilinmu ya ziyarci inda ake sarrafa takin na jabu domin ya gane wa idanunsa abin da ke gudana, ya tarar da wasu buhuna masu nauyin “Kilogram” 50 cike da takin na jabu.

Da yake zagayawa da ‘yan jaridu harabar kamfanin, kwamandan hukumar tsaro ta “Civil Defence” na jihar Neja, Mista Philip Ayuba ya ce labarin da jami’ansa suka samu ne ya kai ga gamo wannan aika-aika da miyagun mutanen ke aikatawa, na zambantan jama’a musamman ma manoma da ke tsananin bukatar takin zamanin.

Ta bakin kwamandan, da samun labarin, sai suka tura jami’ai na musamman domin su lura da abubuwan da ke gudana a wajen, amma da miyagun mutanen suka gane cewa ana lura da su sai suka ranta a na kare suka bar wajen.

Ya kuma ce an riga an rufe filin da ake sarrafa takin na jabu har sai mai wajen ya zo ya fuskanci hukunci, a inda ya bayyana aikin wadannan miyagun mutanen da cewa ba aiki ne na gari ba.

Har’ila yau, ya ce wadannan wasu mutane ne masu neman su yi arziki ko ta halin kaka, amma ya ce hukumar a karkashin jagorancinsa za ta tsananta bincike har sai ta gano wanda ke da wannan ginin.

Ya kuma ce hukumar tsaron ta Civil Defence a karkashin shugabacin Alhaji Abdullahi Jimada Gana tana da aikin da aka tsara mata kuma ba zai yarda ya ci amarnar aikin da aka basu ba.

Bugu da kari, kwamandan ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar Neja da a ko da yaushe su rika taimaka wa hukumar da bayanai game da mutane masu dan hali a cikin al’umma domin a hukanta su, a inda ya ce duk bayanin da aka kawo musu za su yi amfani da shi ne a sirrance.

Ya kuma bukaci jami’an hukumar da su kara himma wajen gudanar da ayyukan su, a inda ya tabbatar musu da cewa hukumar ta rike jindadinsu da muhimmanci.

TAURARUWA