b (1)

Abin al’ajabi ya auku a kauyen Kadna da ke cikin karamar hukumar Chanchaga da ke jihar Neja inda wata matacciyar itaciya ta tashi tsaye gadagau.

Samun labarin itaciyar wacce ta yi shekaru a mace kuma a kwance ya jawo firgita da rudu ga mazauna kauyen wadanda sun dade da sanin itaciyar da ke kusa da makabartar su a mace.

Wannan abin mamaki dai ya faru ne a kauyen na Kadna a ranar lahadi 26 ga watan Yuli 2015 inda mazauna kauyen suka rasa na yi sakamakon jin labarin itaciyar wacce mata suka cinye ta da sara don samun itacen hura wuta ta tashi tsaye kyam!

Tashin itaciyar wacce aka tabbatar da faduwar ta kimanin shekaru biyu da suka wuce ta mayar da kauyen na Kadna dandalin ziyarar masu gani da ido daga  kusa da nesa.

Wani manomi a kauyen Malam Jibrin Usman mai shekaru 20 wanda ke cike da mamakin abin da ya gane wa idanunsa, yace a safiyar ranar da abin ya auku, ya daure daya daga cikin shanunsa biyu a jikin itaciyar kafin ya wuce gona, yace dawowar sa ke da wuya, sai ya ga itaciyar da ke kwance ta mike. A zatonsa, ta mike ne yayin wata iska mai karfi da ta kada a yankin wacce ya dan razana da karfin iskar.

Malam Usman ya karasa da cewa, har shanun sa sun razana a lokacin da iskar ke kadawa domin ya ji suna irin wani kuka na daban.

Ya ce bayan ya dawo hayyacin sa ne ya garzaya da gudu zuwa wajen wan sa Attahiru Usman da ke aiki a gona, ya shaida masa abin da ya gani.

Usman ya ci gaba da cewa, bayan wan sa ya firgita da ganin itaciyar da ta tashi, sai suka koma gida, lamarin da ya tilasta shi yin ta maza, ya dawo don kwance san sa duk da cewa a tsorace ya ke.

Ya ce bayan ya kwance san sa ne ya sake sheka wa da gudu zuwa wata gonar da babban wansu ke aiki, bayan ya shaida masa abin da ya faru ne suka yanke hukuncin su je gida su shaida wa mahaifinsa. Sai dai basu sami damar komawa gonar ba tunda dare ya yi. Amma washe-gari, wato litinin, sai suka kai mahaifin su wajen itaciyar don ya ga abin mamaki.

Gane wa idanunsa ke da wuya sai dattijon ya garzaya wajen mai unguwar su don shaida masa. Shi kuma mai unguwa da ya zo ya gani sai ya shaida ma jam’a abin al’ajabi da ya gani.

Wannan labari dai ya bazu nan da nan wanda ya jawo tururuwar jama’a zuwa kauyen har da wakilan mu da suka ziyarci itaciyar a talatar da ta gabata. Kafin wakilan namu su bar kauyen, sai da suka shaida tururuwa da jama’a suka ta yi zuwa kauyen don ganin wannan itaciya.

Wakilan namu dai sun jiwo daga majiya kwakkwara a kauyen cewar daga cikin maziyartan, wasu sun je ne don kashe kwarkwartar idanun su yayin da wasu sassakar bawon itaciyar ya kai su, sannan wasu na rera wakoki. Haka zalika, wasu sun mai da wurin na yin ibada da surkulle.

Daya daga cikin mazauna kauyen, malam Adamu Zubairu ma ya tabbatar da faduwa da mutuwar itaciyar inda ya shaida wa wakilan mu cewa ko a ranar da abin ya faru, ya bi ta hanyar zuwa gona da safe lokacin da itaciyar ke kwance. Ya ce musu kuma ya san itaciyar a kwance matacciya kimanin shekaru biyu da suka wuce a lokacin da mata kan sare ta jefi-jefi don samun itacen wuta.

Malam Adamu ya kara da cewa, ko Asabar din makon da ya wuce ya ga mata na sarar itaciyar, saboda haka, inji shi, a dauki lamarin daga Allah ne kawai ba tare da danganta shi da wani abu na daban ba. Sannan ya roki wannan abin al’ajabi ya zamo musu na alheri da ci gaba a al’umar su.

Bayan wannan, jama’ar kauyen sun hana sassakar itaciyar don yin siddabaru ko tsubbace-tsubbace don gudun kar hakan ya jawo ma mazauna yankin wata masifa ta daban.

TAURARUWA