unnamed (2)

Gwamnan jihar Osun, Ruaf Aregbesola

Gwamnan jihar Osun, Ruaf Aregbesola ya danganta Kasawar gwamnatinsa wajen biyan albashin ma’aikatan jihar a kan lokaci kan ragin kason da hukumar tsarawa da raba kudaden gwamnati ke aike wa jiharsa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke zanta wa da ‘yan  jaridu a  lokacin da wata kungiya mai zaman kan ta mai suna muryar matan Afrika mai da’awar daukaka mutuncin dan-Adam ta yi a karshen makon nan a Asokoro da ke Abuja.

Alhaji Ra’uf ya ce yana jin zafin rashin iya biyan albashin ma’aikantan jihar a lokocin da ya dace,A cewar sa “ya zama mun wani abu mai matukar wuya in iya biyan alabashi a kan kari sabo da ragowar da muke samu daga kudaden da ake turo mana daga Abuja na wata- wata, ya ce kudin ya ragu da kashi arba’in cikin dari wanda ya haifar da matsala sosai wajen biyan albashin ma’aikatan jiha.

Gwamna Aregbesola ya ci gaba da bayyana cewar har tsananin ya kai lokacin da ya  shiga asusun ajiyan gwamnatin jihar don ganin an biya tarin albashi,amma daga bisani ya kasa.

Ya ce yanzun haka, gwamnati ta ci bashin naira biliyan goma sha biyu don ganin an biya albashi a kan kari ba tare da sake bata wani lokaci ba domin gwamnatin sa na la’akari da walwala da jin dadin jama’a.

Daganan ne gwamna Aregbesola ya  yaba wa kungiyar bisa Karamcin da ta yi masa, sannan ya yi alwashin Kara Kaimi don ci gaba da Kyautata wa jama’arsa.

Ya ce, ya shiga siyasa ne don fitar da jama’ar Osun daga Kangin talauci da yawa da suka sami Kawunan su a ciki.

A yayin bayar da kyautar,shugaban kungiyar Hajiya Amina Idris ta ce sun bashi Kyautar ce don yaba kyuatata wa alumma da ya ke yi.

A cewar ta, “wannana Kyauta ta yabo,mun baka ne saboda saduakar da kai da ka yi wajen Kyautata wa al’umarka.”

Ta ce gwamna Aregbesola ya zame wani tauraro wajen taimakawa ilimin yara da kuma taimaka wa al’umma baki daya wajen cimma muradeen su.

TAURARUWA