Wani matashi dan shekara 30 da haihuwa a duniya wanda ke sana’ar kabu-kabu mai suna Garba Adulrahman ya shiga hannun hukuma, watau ‘yan sanda; ana tuhumarsa da laifin yiwa wata yariya ‘yar shekara biyu da haihuwa fyande a wata unguwa da ake kira Somolu a jihar Ikko.

A cewar dan’uwan wanda ake tuhumar wanda ya yiwa ‘yan jarida bayani yace wannan al’amari ya auku ne ranar sati 21 ga watan faburairu na wannan shekara da   misalin karfe goma sha  daya na safe. Yace uwar yarinyar tana zaune ne a Gbagada.Ya ce, uwar yarinyar ta kai wa kanwarta ziyara a unguwar su ne

sanadiyyar haka  diyarta ta bace wanda ya sa aka shiga yawon neman ta.

Ana cikin haka ne sai wani bawan Allah yace ya fa ga Garba Abdulrahman a  kan babur da wata yarinya ya  na faman gudu. Daga nan ne aka shiga neman yariya daga  bisani wasu  ayarin mata suka gano  Abdulrahman amma kuma babu wanda ya san inda yarinya take.

Bayanin ya kara da cewa a lokacin da ayarin matan suka shiga gidan Abdulrahman ya ki ya nuna musu inda ya boye  yarinyar, anan ne kanwar uwar yarinyar ta yi fushi har ya kai ga ta tokare shi a ciki bayan wani sa-in-sa da ya shiga tsakaninsu da wanda ake tuhuma da laifin.

A cewar bayanin Abdulrahman ya yi barazanar aika wani mugun abu, ya kuma ce duk wacce ta zo kusa da shi zai sare ta da adda, wanda a hakan ya sa suka kai kara wajen ‘yan sanda.

A lokacin da ‘yansanda suka iso wajen sai suka fara bincikken dakunnan dake cikin wajen, kwatsam! Sai suka hango yarinyar a cikin wani babban kwano da ake tara ruwa, a wannan lokacin ko tafiya bata iya yi saboda ta galabaita. Da zarar ta yi tafiya kadan sai ta fadi, a lokacin yansanda ba su yi tunannin Abdulrahman ya shigi yarinyar ba sai da daya daga cikin  ‘yan sanda ya duba kanfanta tare da kayan da ta sanya, an wanke suna shanye, yayinda wanda a ke tuhumar bai sanye da komai a jikinsa.

Bayanin ya kara da cewa ‘yan sanda a take suka dauki matakin wuce wa da yarinyar zuwa Asibiti don ganin likita wanda zai duba yarinyar inda daga bisani ya tabbatar da cewa lalle Abdulrahman ya yi wa wannan yarinya fyade.

Bayan da ‘yan sanda suka kammala binciken su suka tura shi kotun majistare da ke Ebute Meta ana tuhumarsa da laifuka hudu.

Abdulrahman ya ki ya amsa cewa ya yi wa yarinyar fyade kuma yace ma bai san mutanen da suka kawo shi kara kotu ba.

Daga bisani kuma yace mutanen sun ce ne ya taimaka musu  a wajen daukan yarinyar a kan babur dinsa saboda kaya da ya yi musu yawa, hakak dai ya yi ta kame-kame inda ya ce dalilin da ya sa ya yi wa wadannan gungun matan barazana da adda bayan ya jefe su da duwatsu kenan.

Jami’in yan sanda mai gabatar da kara Richard Odige ya bayyanawa kotu cewa wannan laifin ya sabawa sashi na 267 da 137 da 170 da kuma 56 na kundi shari’a na jihar ikko.

Inda ya kara da cewa yana tunanin wanda ake tuhumar bai san abinda ya ke fadi ba, ganin irin maganganun da ya yi ta fadi.

TAURARUWA