AUWAL BOJOH

Daga Awwal Umar Kwantagora

Tsohon shugaban karamar hukumar mulki ta Rafi da ke jihar Neja, kuma tsohon shugaban kungiyar shugabannin karananan hukumomin Najeriya, Hon. Garba Tanko Bojoh, ya zama Sardaunan wakilin Minna.

Nadin nasa ya biyo bayan jajircewarsa wajen taimakon jama’a da kokarinsa na ciyar da kasa gaba kamar yadda fadar Wakilin Minna ta ambata a takardar amincewa da shi a matsayin Sardaunan wakilin minna.

Takardar ta ce sabon Sardaunan wanda shi ne nadinsa na farko da aka gudanar a fadar ranar asabar 7 ga watan Disamba, 2019, ta ambata cewar Alh. Garba Tanko Bojoh ya taka rawar gani wajen daga martabar kungiyar shugabannin kananan hukumomi wanda ba a taba samun irinsa ba.

Takardar ta ci gaba da bayyana cewar irin namijin kokarin da ya yi lokacin yana shugabantar karamar hukumar Rafi, wajen samar da ruwan sha da tabbatar da tsaro a yankin, hakan ya sa ya cancanci wannan matsayi domin zai iya kare martabar fadar Wakilin Minna kamar yadda ya nuna a baya.

Fadar ta jawo hankalin Sardaunan da ya kara jajircewa wajen ayyukan alheri da zai kara kare martabarta a cikin kowane yanayi; domin haka ne ma fadar ta taya sabon Sardaunan murnar samun wannan matsayi.

Jama’a da dama daga karamar hukumar Rafi sun yi farin cikin samun wannan sarautar na Hon. Garba Tanko Bojoh.

TAURARUWA