AUWAL GWAL Kwamred Musa Adamu Nasko.

 

Daga Awwal Umar Kwantagora

Shugaban kungiyar masu hako ma’adanai na karkashin kasa reshen jihar Neja, Kwamred Musa Adamu Nasko ya bayyana cewar jihar Neja na da dangogin ma’adanan karkashin kasa har kasha takwas idan ka debe Zinare da aka fi mayar da hankali a kanta wanda sama da shekaru hudu gwamnatin ba ta mayar da hankali a kan yadda za ta amfana da su ba.

Kwamred Nasko ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Tauraruwa a garin Minna, babban birnin jiha.

Ya cigaba da cewar a kullum ana dibar tan biyu na Zinare a sassan jihar wanda ake fita da su a gwamnatance bisa umurnin gwamnatin tarayya banda wanda ake safararsa ta barauniyar hanya, amma duk da haka gwamnatin jiha ba wani abinda take amfana da shi ta fannin kudin shiga.

 Acewar Nasko, idan gwamnatin jiha ta mayar da hankali za ta rika samun kudaden shiga da za ta iya yin ayyukan raya kasa da su kamar dai yadda ya dace.

Da ya juya bangaren shugabancin kungiyar kuwa, Nasko ya ce a yanzu haka sun zo da sabon tsarin yadda leburori za su iya amfana da kudaden da ake biyansu da shi, ta hanyar sanya idanu kan duk wani kamfanin da ya baiwa lebura aiki za ta biya shi hakkinsa kamar yadda ya dace, domin ba za su sake barin ana karkatar da kudaden leburori ta hannun wasu da ke zaune suna ci da gumin lebura ba.

Ya yi kurarin cewa lokaci ya yi da leburori za su hadu domin kafa kungiyoyi ta yadda za su rika amfana da tallafin da gwamnatin tarayya ta sha alwashin baiwa leburori na kayan aiki da kudade ta fuskar inganta rayuwarsu, wadannan kudaden ba za a baiwa mutum daya ba dole sai ta hanyar kungiyoyin hadin-gwiwa domin ta haka ne kadai mai karamin karfi zai iya amfana da tallafin. Inji shi.

Nasko ya jaddada cewar jami’an tsaro sun mayar da masu hakon ma’adanan kasa saniyar-tatsa ta hanyar kamo su ana garkamewa a gidajen Yari har sai sun yi belin kansu da makudan kudade.

Masu hakon kasa ba ‘yan ta’adda ba ne, jami’an tsaro ba sa shiga daji don ganewa idanunsu abinda ke faruwa. Ba wani leburan da zai tafi ya kama hakon kasa sai da umurnin gwamnati, don haka ya yi nuni da cewar ba za a cigaba da sanya idanu hakan na cigaba da faruwa ba.

“Bisa rajistan da muke da shi, muna da mambobi sama da dubu dari biyar, amma yanzu za mu sake tantancewa kuma duk wanda ya cika ka’ida za mu ba shi takardar shaida, dole ne kowa ya ba da cikakken bayaninsa sannan ya samu fitaccen mutum da zai tsaya masa ta yadda idan aka samu mutum da laifi za a samu saukin kamo shi domin mika shi ga jami’an tsaro. Kamar yadda muka samar da shugabancin jiha haka za mu kafa shugabanci a sauran sassan kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar nan.” A ta bakin shugaban.

 

 

TAURARUWA