CHANJA-SHI-MALAM

Malam Aliyu Zakariya (Canja Shi Malam) matashin malamin addinin musulunci ne da ya tsunduma cikin harkar siyasa, yana daga cikin matasan da suka shiga siyasa da kafar dama, ya taba takarar kujerar majalisar dokokin jihar Neja, kuma a yanzu shi ne dan takarar shugabancin karamar hukumar mulki ta Kwantagora a inuwar Jam’iyyar PDP.

A tattaunawarsa da Awwal Umar Kontagora, ya yi tsokaci ne kan kudaden shigar kananan hukumomi da hanyar da ya kamata a bi wajen amfanar da jama’a da wadannan kudaden.

A sha karatu lafiya:-

Tauraruwa: – Farko dai ana ta cece-kuce dangane da baiwa kananan hukumomin kasar nan ‘yancinsu hanyar ba su kudadensu kai-tsaye daga susun gwamnatin tarayya, shin ya kake kallon wannan lamarin.

Canja shi Malam: – Da farko dai ina godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya bani dama har jam’iyyar PDP ta bani tikitin tsayawa takara, sannan ina godiya a kan damar da wannan jaridar ke ba ni a kowane lokaci.

Maganar baiwa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye abu ne mai kyau, domin shi ne zai dawo da martabar dimukuradiyya, a baya an yi yunkurin rushe kananan hukumomi saboda rashin katabus din da ba sa yi, wanda tun farko ba laifinsu ba ne, wasu gwamnonin ne suka jefa su a wannan halin.

Gudu-ba-hanzari ba; su kansu shugabannin kananan hukumomin sun taimaka wajen hana al’ummarsu abinda ya dace; Kananan hukumomi na samun kudaden shiga na cikin gida, me suke yi da su? wanda idan ka bincika ana kashe kudaden ne ta hanyoyin da ba su dace ba, wanda kowane shugaban karamar hukuma yana kallon irin wadannan kudaden kamar kudin aljihunsa ne, sun manta cewar an karbi kadin ne a hannun jama’a da nufin yin aiki da su amma ba sa yi.

Idan ba a iya sarrafa ire-iren wadannan kudaden yadda ya kamata ba, to ko da kudi masu kauri suka shigo aljihun karamar hukuma, haka za su tafi ba su san aikin da suka yi da su ba, alhalin kuwa akwai gyaran magudanan ruwa, akwai samar da kayan aiki ga kananan asibitocin da ke karkara, ga maganar samar da ruwan sha ga jama’a, ka ga duk abubuwa ne masu muhimmanci, amma an zauna ana fadin gwamna bai bada kudin gudanar da aiki ba, wannan kuskure ne babba.

Tauraruwa: – Malam, akwai maganar samar da babbar kasuwar hatsi a yankin karamar hukumar Kwantagora a ‘yan shekarun baya; Ya kake kallon wannan shirin?

 Canja shi Malam: – Gaskiya! wannan kuduri ne mai ma’ana idan dai har an yi la’akari da kasar Kwantagora, domin noma da kiwo, kasuwanci su ne muhimman abinda muka dagara da su a karamar hukumar nan, kuma su ne suka baiwa baki damar miqe kafa saboda kasar na da albarka. Da a ce gwamnatin jiha tare da karamar hukuma sun mayar da hankali an samar da shi; ala-kulli-halin, da kudurin gwamnatin tarayya na inganta harkar noma ya kara inganta, saboda zai taimaka wa kananan manoma wajen daraja abinda suke nomawa saboda ko a yanzu kana ganin yadda ake safarar abinci zuwa wasu makwabtanmu har da wasu kasashen da ke makwabtaka da mu. Kuma zai taimaka wajen samun karin kudaden shiga ga karamar hukumar baya ga samar da ayyuka ga dimbin matasa.

Tauraruwa: – Jam’iyyar PDP ta kwashe shekaru 16 tana mulkin karamar hukumar nan, shin akwai wasu abubuwan da kake gani da za ka ce wani abin cigaba ne ta bar muku?

Canja shi Malam: – Tun farko dai, rikicin siyasa da ya dabaibaye yankin ya sa an kona sakatariyar karamar hukumar wanda hakan ya haifar da aka sake mata matsuguni zuwa wajen gari. A lokacin da Dakta Mu’azu Babangida Aliyu ya dare bisa karagar mulkin jihar Neja a a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP, ta gyara duk wuraren da aka barnata, ita ce kuma ta samar da tagwayen hanyar da aka dade ana nema a cikin garin Kwantagora, tun bayan mulkin Shehu Shagari ba a sake gina gidajen gwamnati ba sai zuwan mulkin Talban Minna, inda ta gina gidaje guda dari, akwai ayyuka da dama da ba za su fadu ba a cikin wannan dan takaitaccen lokaci da gwamnatin Talba ta yi.

Idan kuma ka dawo bangaren karamar hukuma, a lokacin mulkin Talba ne Kwantagora ta sami hanyoyin cikin gari da dama da har yanzu ana amfana da su, wanda gwamnatin da ta gaje shi, ita kuma ta dora a bangaren ruwan sha ta hanyar kafa fanfunan burtsatse da kuma samar da guraben aiki ga al’umma.

Tauraruwa: – Ana yi maka lakabi da canja-shi Malam, shin me za ka ce wa matasan Kwantagora ganin tana daya daga yankin da ake ganin ta zama zakaran gwajin- dafi a bangaren siyasar ‘yanci.

Canja shi Malam: – Matasa su ne kashin bayan kowace irin gwamnati, a wannan karon muna da kudurin tafiya da kowa, dan haka kuma ina kira ga matasa musamman ganin lokacin zabe na kawo jiki, da kar su bari ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen tayar-da-zaune-tsaye, su zama wakilanmu na gaskiya wajen ganin an yi siyasa mai tsafta wajen sanya ido a lokacin zabe, idan ka duba, yau su ne ke bin gida-gida wajen tallata ‘yan takara, to ya dace kuma kowa ya zama jami’in sanya ido wajen ganin ba a yi magudi ko murdiyar zabe ba.

A Kwantagora, mu ne muka kawo akidar a-kasa a-tsare kuma a-raka, wannan akidar tana nan har yanzu. Kowane matashi ya zamo garkuwan kare siyasarmu ta hanyar hana murdiyar zabe, su ki amincewa da bangar siyasa, su kuma kare mutuncin karamar hukumarmu. Idan mun cigaba da wannan akida, ina da tabbacin cewar a karamar hukumar Kwantagora zamu sami jagoranci mai inganci, jagorancin da kowa zai yi na’am da shi.

Tauraruwa: – A karshe, ya Malam yake kallon yadda zabe zai kasance.

Canja shi Malam: – Zabe za a yi shi lafiya da yardar Allah, domin mai girma gwamna ya yi alkawarin baiwa kowace jam’iyya ta yi nasara kujerarta, kuma ita kanta hukumar zabe a yanayin da take ciki muna kyautata zaton adalci daga gareta. Ka sani kuma mulki na Allah ne kuma gare shi muka dogara, saboda haka jama’a kowa ya tabbatar da ya mallaki katin zabensa domin jefa kuri’arsa a inda ya dace, mu zauna lafiya da kowa kuma mu kare hakkin juna.

Tauraruwa: – Canja shi Malam, muna godiya.

Canja shi Malam: – Madallah, Allah ya kara daga darajarku. Nagode.

 

TAURARUWA