baqon-dauro

 

Daga Muhammad Awwal Umar

Babban darakta a hukumar kula da lafiya a matakin farko na qasa, Dakta Faisal Shu’aib ya bayyana cewar gwamnatin tarayya da ma’aikatar lafiya ta qasa sun sha alwashin daqile barazanar cutar baqon-dauro da ciwon zazzabin cizon sauro mai tsanani.

Daraktan ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya da ya gudana a jihar Kano. Ya ce qungiyoyin UNICEF da WHO da kuma hukumar kula da daqile cututttuka ta qasa suna aikin hadin guiwa wajen bada rigakafi ga cutar zazzabin cizon sauro mai tsanani da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a jihar Bauchi, da kuma yunqurin daqile rahoton bullar cutar baqon-dauro da ya bulla a jihar Kano.

Yace sun gabatar da yekuwar wayar da kan jama’a dangane da allurar riga-kafi kashi na biyu daga ranar 14 ga watan Nuwamba zuwa 19 ga watan da ya shafi jahohi sha bakwai na qasar nan, inda suke da qudurin yi wa yara ‘yan watanni 12 zuwa 24 allurar.

Ya ce riga-kafin za ta kare yara miliyan 2-3 daga mutuwa domin yana daya daga cikin hanyoyin da za a kare yaduwar cututtukan, kusan yara miliyan uku ke mutuwa a kowace shekara sakamakon cututtukan cizon sauro mai tsanani, baqon-dauro da yunwa da ke addabarsu a ‘yan qarancin watanni da haihuwa.

A Najeriya, akwai magunguna kyauta a asibitocin gwamnati, wannan shekarar mun samu rahoton bullar cutar cizon sauro mai tsanani ( Shawara) a jihohin Katsina da Bauchi da Ebonyi, sai kuma baqon-dauro a jihohin Yobe da Barno da Kaduna.

Gwamnatin Najeriya da hukumar kula da lafiya a matakin farko wato NPHCDA da abokan hadin guiwar su kamar UNICEF da WHO, US CDC sun sha alwashin hada hannu wajen ganin an kawar da wannan barazanar a cikin al’umma don ceto rayukan qananan yara.

Wannan qudurin na cikin shirin hukumar lafiya na ceto rayukan yara qanana daga shekara daya zuwa biyar a qallan miliyan 22.2 daga mutuwa, a jihohi sha tara har da Abuja.

A jihar Kano kawai daga watan Oktoban da ya gabata zuwa yanzu ana sa ran yi wa yara qanana allurar a qallan miliyan 2.5 a dukkanin qananan hukumomi 44 da ke jihar.

Dakta Faisal yace aikin zai gudana ne qarqashin kulawar hukumar NPHCDA tare da hadin guiwar qungiyoyin GAVI, da UNICEF, WHO da CHAI, US CDC da AFENET NSTOP.

Za a dai ci gaba wannan aikin har sai an tabbatar da duk qaramin yaron da ya kamata ya samu wannan allurar rigakafin ya same shi

 

 

 

Situation Room, YIAGA demand cancellation of Kogi poll

Ex-President Goodluck Jonathan and his wife, Patience Jonathan, cast their votes at ward 13, polling unit 39 in Otuoke, Ogbia local government area of Bayelsa State, at about 11:30am on Saturday, November 16.

TAURARUWA