Daga Muhammad Awwal Umar

Jibo Kuta

Shugaban qungiyar masu sana’ar niqa da surhe ta jihar Neja, Alhaji Muhammadu Jibo Kuta

An bayyana sana’ar niqa da surhe a matsayin sana’ar da ta samo asali a rayuwar dan- Adam. Shugaban qungiyar masu sana’ar niqa da surhe ta jihar Neja, Alhaji Muhammadu Jibo Kuta ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai kafafen yada labarai a Minna fadar gwamnatin jihar Neja.
Jibo Kuta ya cigaba da cewar ganin yadda rashin aikin yi ya zama ruwan dare, yanzu haka qungiyarsu ta quduri aniyar mayar da hankali a manyan ayyuka guda uku, da suka hada da koyar da matasa sana’ar niqa, bayar da dama ga wadanda suka manyanta kuma suke muradin sana’ar ta hanyar dora shi a inda zai iya cin moriyar sana’ar, na uku kuma yanzu haka qungiyar ta bada dama ga wanda ke da kudi kuma yana son sanya hannun jari a qungiyar ta yadda qungiyar ce za ta dauki nauyin kula da jarin ta yadda mai dukiyar zai iya cin moriyar ribarsa da dukiyarsa ke janyowa a qarshen kowane wata.
Yanzu haka dai, idan ka cire wadanda ba su yi karatun boko ba, da wadanda karatunsu bai yi nisa ba; haka kuma, a kowace shekara ana samun matasa dubu saba’in da biyar dake kammala karatun jami’a wanda dubu sha biyar ne ke iya samun aiki a hannun gwamnati da wasu kamfanoni, wannan matsalar na rashin aiki ga matasa ya fi matsalar Boko Haram illa a cikin al’umma. Rashin aiki babban matsala ne a rayuwar matasa da al’ummarmu da cigaban tattalin arzikin qasa.
Da yake qarin haske ga wakilinmu, shugaban qungiyar a Neja ta tsakiya, Malam Usman Yakubu, ya ce a yankinsu babban matsalar da suke fuskanta bai wuce matsalar wutan lantarki ba, duk da cewar kusan kashi saba’in da biyar na wutan lantarki daga yankinsu ake tatsarsa.
Zamani ya zo da kusan komai ya ta’allaqa ne a kan wutan lantarki, don haka “muna kira ga gwamnatin jihar Neja da kamfanonin da ke samar da wuta a jihar nan da su inganta shi.” Ya qara da cewar “wannan sana’ar ta samar wa jama’a da dama rufin asiri, qungiyarmu tana shiga ta yi ruwa da tsaki domin warware matsalolin da suka shafi wutan lantarki wanda bai fi qarfinmu ba, kuma ita kanta gwamnati na qaruwa da mu wajen samar da kudin shiga.” 
Da yake bayani a madadin kafafen yada labarai, babban darakta a kamfanin buga jaridun Newsline Newspapers da Tauraruwa, Malam Ndama Abubakar, ya ce qungiyar dai duk da kasancewarta jaririya ce, ta zo da manufofi nagartattu da kafafen yada labarai za su yayata shi, musamman rayuwar mutumin da ya bar aiki abu ne mai kyau ya samar wa kansa madogara.

 

TAURARUWA