Daga Muhammad Awwal Umar

IMG-20170115-00338

Shugaban qungiyar masu surhe da niqa ta qasa reshen jihar Neja, Alhaji Muhammadu Jibo Kuta

An yi kira ga gwamnatin Jihar Neja da ta hada hannu da masu sana’ar surhe da niqa domin cike gurabun ayyuka ga matasa. Shugaban qungiyar masu surhe da niqa ta qasa reshen jihar Neja, Alhaji Muhammadu Jibo Kuta ne ya yi wannan kira jim kadan da rantsar da shi a matsayin shugaban qungiyar ta jiha.
Alhaji Jibo Kuta ya yi nuni da cewar qididdiga ya gano cewar sama da matasa dubu saba’in da biyar ne ke kammala karatun digiri a qasar nan wanda da wahala a samu dubu ashirin da biyar da ke samun aiki bayan sun kammala karatun.
Ya ce, idan dai har gwamnati za ta mara wa qungiyar baya; to kuwa babu shakka za ta iya samar wa dimbin matasa gurabn aiki a sana’ar niqa da surhe, bugu da qari ma, akwai matasa da dama da ke zaune kara zube babu aikin yi, wanda wasunsu ba su je makaranta ba, wasu sun je makarantar ba su samu damar kammalawa ba saboda rashin qwazo ko wani dalili na daban, wannan qungiya ta quduri aniyar samar da gurabun aiki ga matasa maza da mata masu tasowa.
Shugaban ya qara da cewar “ina jawo hankalin gwamnati da masu hannu da shuni wajen taimaka wa jama’a, musamman ma a Arewacin qasar nan domin kawar da zaman kashe wando ga matasan, sana’ar niqa da surhe sana’a ce ta rufin asiri, ina da yara da suka kammala karatu yanzu haka; kuma da wannan sana’ar na riqe su na rene su har suka kai ga wannan matsayi na ilimi.”
“Babban matsalar da ke yi wa wannan sana’a illa, ita ce ta wutan lantarki da tsadar man dizal, lallai shugaban qasa na qoqari wajen inganta wutan lantarki, duk da haka, muna son gwamnati ta qara qoqari a kai, domin a sana’ar nan muna da masu surhe da kuma mata masu bakace, ka ga banda wanda ya zuba dukiyarsa; akwai wasu da ke labe suna amfana da sana’ar. Ya kamata gwamnati ta qara mana qwarin gwiwa ta hanyar tsaya mana a bamu rance domin inganta sana’ar, wannan qungiya ita ce ta farko a jihar nan har ma a qasa baki daya, mun fito da kyakkyawar niyya wajen samar da aikin yi ga jama’a tare da habbaka hanyoyin samar da kudin shiga ga ita gwamnatin.” In ji sabon shugaban.
Da yake qarin haske, Hakimin Maikunkele da ke gundumar Bosso, Alhaji Sulaimanu Abdullahi Dada ya ce lallai samuwar irin wadannan qungiyoyi alheri ne ga qasa, domin masu sana’a ne suka amince su hadu kan manufa daya domin taimaka wa qasa, jama’a na qaruwa da su sosai kuma ita kanta gwamnati tana qaruwa da su domin su na saye, su na sayarwa. Kuma a kowane lokaci, akwai wadanda ke rabe da su kuma suna amfana.

Barista Gambo Gwada, shi ne lauyan da ya rantsar da sabbin shugabannin, a cikin wata tattaunawa da na yi da shi, ya ce lallai wannan qungiya ta zo da manufofi masu ma’ana, domin haduwarsu waje daya zai taimaka wa gwamnati samun sauqi a duk lokacin da wata matsala ta taso.

A kwanan nan ne qungiyar ta tsaya tsayin daka wajen ganin an samu qarin tarasfoma na wuta a Kuta, sa’annan idan ka dubi shugabancin, bai tsaya a jiha kawai ba, ya qunshi shiyyoyi ne da qananan hukumomi, hakan zai bada damar sanin irin matsalolin da suke fuskanta da yadda za a samu sauqin dinke su.
Barista Gwada ya jawo hankalin gwamnati wajen jawo ire-iren wadannan qungiyoyi a jika domin samun nasarar sauqaqa rayuwar al’umma, masu sana’ar surhe da niqa akwai gudunmawa da suke bayarwa sosai a rayuwar al’umma.
Taron rantsuwar da ya samu baquntar mafi yawan masu sana’ar surhe da niqa a dukkanin qananan hukumomi ashirin da biyar da ke jihar, an rantsar da sabbin shugabanni na jiha da na shiyya da kwamitin ladabtarwa da kuma masu bada shawara.

 

TAURARUWA