Daga Muhammad Awwal Umar

mohammed babangida

Babban darakta mai kula da Makarantar El-Amin Internation School, Dokta Muhammed Babangida

An bayyana cewar baiwa matasa ilimin zamani da na addini shi ne zai a za su a turba madaidaiciya ta rayuwa, wanda hakan bai yiwuwa sai masu hali sun taimaka wajen zuba dukiyoyinsu domin farfado da rayuwar matasa a qasar nan.

Babban darakta mai kula da Makarantar El-Amin Internation School, Dokta Muhammed Babangida ne ya bayyana hakan a ofishin shi lokacin da wani matashi mai rajin zaman lafiya a duniya “DUDUWALE TREK FOR WORLD PEACE” ya ziyarce shi.

Dokta Muhammed ya cigaba da cewar mahaifiyarsu mai rasuwa (Dokta Maryam Babangida) uwargidan tsohon shugaban qasa a mulkin soja, Janar Babangida ta kafa wannan makaranta kuma ta kafa shi ne da zimmar taimaka wa ‘ya’yan marasa qarfi wajen ba su ilimi da taimaka wa rayuwarsu ta yadda zai inganta, kan haka suka kafa gidauniya ta yadda kowa ma zai iya bada nashi gudunmawa wajen ceto ilimi musamman a yankin Arewacin qasar nan ganin yadda aka yi masu zarra. Don haka, wannan makaranta za ta dauki qudurce-qudurcen da wannan matashin ya kawo domin shigar da shi a manhajar karatunsu don nuna wa matasa masu tasowa muhimmancin taimako ta hanyar ilimi da yadda za a iya ceto rayuwar al’umma daga halin da suke ciki.

Da yake amsa tambayoyin manema labaru, Duduwalle ya ce ya taso ne daga jihar Adamawa wanda nan ne asalinsa ya ratso ta jihar Gombe da Bauchi, ya zo Kano da Kaduna inda ya zanta da wasu hukumomin gwamnati da qungiyoyi masu zaman kansu domin nuna masu muhimmancin zaman lafiya.

Ya ce a shekarun baya, babu inda ya fi Arewacin qasar nan zaman lafiya, amma yanzu duk kusan qasar da nahiyar Afrika babu zaman lafiya, wanda hakan ke zama dalilin salwantar rayuwar matasa da dama. Ya ce “ya kamata gwamnati da qungiyoyi masu zaman kansu su tashi tsaye wajen nuna wa jama’a muhimmancin zaman lafiya, wannan tattakin da muke yi, muna yin shi ne da manufa, manufar tamu kuwa ita ce wayar da kan jama’a a kan muhimmancin zaman tare da hanyar fahimtar juna, don haka ya kamata shugabanni su sani muddin babu zaman lafiya, to kuwa tattalin arziqin qasa ma wargajewa yake yi, don haka yana da kyau a zauna a lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen rage kaifin gaba da qiyayya da yayi katutu a cikin zukatan al’umma.”

Ya ce babban burinmu shi ne tabbatar da hadin kai tsakanin al’ummar Najeriya da Afrika. Yaqi da shan miyagun qwayoyi a cikin al’umma. Jaddada muhimmanci neman ilimi ga matasa maza da mata. Farfado da kyawawan al’adu da dabi’u na qabilun Najeriya. Kawar da cin hanci da rashawa, nuna bambancin addini ko qabila.

Muddin muka samu nasara a kan wadannan; to kuwa lallai ne zaman lafiya zai iya dawo da gindinsa a wannan qasa, saboda haka, ya kamata gwamnati ta daina amfani da siyasar addini wajen rarraba kawunan ‘yan qasa.

Duduwalle ya qara da cewar lallai manufa da muradun wannan gidauniya ta El-Amin Foundition abin a yaba ne, a don haka, ya jawo hankalin Dokta Muhammed Babangida da su qara qaimi wajen tabbatuwar wannan nufin nasu kasancewar su na da hanyoyin taimakawa kamar yadda ya gani.

TAURARUWA