Daga Muhammad Awwal Umar

1(6)

Kwamishina a ma’aikatar yada labaru da yawon bude ido, Mista Jonathan Tsado Vatsa

Gwamnatin Jihar Neja ta nuna rashin amincewarta kan yadda wasu dillalan abinci ke wawushe kayan abinci sun a boyewa, wanda a cewarta wannan bala’in na iya janyo barazanar rashin wadataccen abinci a cikin qasa.

Kwamishina a ma’aikatar yada labaru da yawon bude ido, Mista Jonathan Tsado Vatsa ne ya bayyana hakan a yayin wani rangadi da ya kai a wasu kasuwannin hatsi a jihar.

Mista Vatsa ya ce, mummunar dabi’ar boye abinci ba alheri ba ne a qasa, Jihar Neja na daya daga cikin jahohin da suka noma abinci mai dimbin yawa, amma ‘yan jari hujja sun baza komarsu a kasuwanni wanda hakan na iya kawo naqasu ga jama’a wajen ganin sun amfana da amfanin gonar da aka samu a wannan shekarar.

Kwamishinan ya shawarci al’ummar jiha da su sanya kishin qasa gaba na samar da wadataccen abinci akan manufarsu na samun qazamar riba ta hanyar boye abinci. “Ba za mu lamunci dillalai su riqa zuwa suna saye abincinmu su boye sai ya yi tsada kafin sunfitar das hi ba, alhalin manoman ba su ci amfanin noman da suka yi ba; kuma an jefa su cikin halin quncin rayuwa.” In ji Vatsa.

Mista Vatsa ya yaba wa jama’ar jihar ganin irin halin quncin rayuwa da ake fuskanta bai hana jama’a suka rungumi manufofin gwamnati sau da qafa ba, don haka gwamnati ta bullo da hanyoyin da jama’a za su samu sauqin rayuwa ta hanyar farfado da qananan sana’o’i a kasuwanninmu.

 

TAURARUWA