Daga Muhammad Awwal Umar 

david umar

Sanata mai wakiltan Neja ta Tsakiya, Sanata David Umaru

An bayyana maganganun sanata mai wakiltan Neja ta Tsakiya, Sanata David Umaru a matsayin maganganu masu buqatar raba kawunan jama’a. A wata takarda da qungiyar dattijan Gwarawa ‘yan asalin jihar Neja ta fitar, ta ce maganganun sanatan bai tattare da komai face qoqarin cimma wata manufa ta qashin kai wanda wannan ba shi ne wakilcin da suke buqata ba.
A cewar takardar, tun dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999, sai a wannan gwamnatin na APC ne qabilar Gwari ta samu muqamin minista, bayan haka a jihar Neja suna da qabilar Gwari da ke riqe da muqamin kwamishina har guda hudu, haka kuma,shugaban hukumar kula da daukar ma’aikata ta jiha, qabilar Gwari ne, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jiha, Gwari ne, shugaban hukumar kula da qananan hukumomi, qabilar Gwari ne, shugaban majalisar dokokin jiha ma Gwari ne, babban mai baiwa gwamna shawara akan harkokin siyasa,  qabilar Gwari ne, mataimaki na musamman akan harkokin siyasa ga gwamna, Gwari ne. Idan ko har Gwarawa sun samu irin wannan daman me Sanata David Umaru yake nema a siyasa, idan wannan bai zama cigaba ba to lallai akwai lauje cikin nadi.
Takardar wadda ta samu sa hannun Alhaji Awaisu Muhammadu Giwa da Muhammadu Inuwa Kilishi Guni, sai kuma Adamu Gurmana da Ataza Paiko, ta ci gaba da cewar lokacin da sanatan ke yaqin neman zabe, ya yi wa al’ummar qauyukan Manta/Gurmana alqawarian cewar idan aka zabe shi zai tabbatar ya an biya su kudinndiyya na wadanda aikin samar da lantarki na Zungeru ya shafa wanda har zuwa yau ba wanda ya sake jin duriyarsa.

Bayan samun matsalar sojoji da gwarawan Gupa, ba wani gudunmawa na abinci ko kudi da sanatan ya bayar a matsayin shi na mai wakiltar wannan yankin, bayan an qona gidajensu da abincin da suka noma har kudaden da suka kashe domin bin haqqoqinsu ba wani gudumawar kudi da sanatan ya bayar a matsayin tausayawa.
Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, Alhaji Awaisu Muhammad Giwa ya ce bai kamata sanatan ya fake da guzuma yana harbin karsana ba, domin lokacin siyasar qabilanci da bambancin addini ya wuce, ana siyasa ce ta hikima da hankali. Bai kamata mai riqe da irin matsayi na wakilcin jama’a ya riqa fitowa yana maganganun da ba su da kan gado balle makama ba.

Mu dai a iya saninmu, jam’iyyar APC da gwamnatin jiha bisa jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello ta mutunta Gwarawa kuma ta ba su matsayin da ya dace, fitowa kana cewar wai gwamnati na danne qabilar gwarawa ba gaskiya ba ne.
Muhammadu Inuwa Kilishi Guni wani dattijo a qungiyar, ya ce idan aka yi la’akari da irin kudaden da Sanatan ya karba a matsayin kudin ayyukan raya qasa, ya fito ya fada wa al’ummar Gwarawa yadda ya kashe kudaden da irin ayyukan raya qasa da ya yi da zai zama mai alfanu ga qabilar Gwari. Sanata Dahiru Awaisu Kuta mai rasuwa a dalilinsa an kafa hukumar kula da yankunan da ke kusa da madatsun ruwa, ta yadda za a inganta rayuwarsu da kudaden shigar da ake samu daga kamfanonin da ke samar da wutan lantarki a jihar, tun bayan rasuwarsa duk da an kawo cibiyar a Minna, fadar gwamnatin jihar Neja, me Sanata David Umaru ya yi domin ganin shirin bai durqushe ba.
“Mu qabilar Gwari kan mage ya waye, kanmu daya ba zamu sake yadda ana amfani da sunan Gwari don cimma wata manufa ta siyasa ba, abinda muke gani a wasu maqwtan jahohi na siyasar addini da qabilanci ba zamu yadda ya zo jihar Neja ba. Don haka ina fadi da babban murya ga abokan zamanmu, ba mu amince da siyasar qabilanci da addini ba a jihar nan ba da sunan qabilarmu ba, idan sanata bai daina irin wadannan maganganun ba na kawo rarrabuwar kawuna, lallai za mu yi amfani da jama’armu wajen dawo da shi gida.
Martanin dai ya biyo bayan kalaman Sanatan ne a taron bukin al’adun gargajiya da aka gudanar a Gurara, inda sanatan ya zargi gwamnatin jiha da danne qabilar Gwari, inda ya cigaba da cewar gwamnatin jiha tana qoqarin danne qabilar Gwari wanda ko muqaman kirki ba ta baiwa ‘yan qabilar ba.

TAURARUWA