Daga Garba Bello

gov sani bello

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya jinjina wa hukumar kula da jin dadin Alhazai da kuma tawagar Amirul-Hajji ta jiha, saboda kwazon da suka nuna wajen gudanar da aikin Hajjin bana kuma har suka sami damar samo hanyar takaita yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da hidimar aikin Hajji a duk shekara.

A can baya dai, gwamnati na batar da zunzurutun kudi da yawansu ya haura naira bilyan biyu; wanda a yanzu abin ya sauko zuwa naira milyan dari biyar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karban rahoto daga hannun kwamitin Amirul-Hajj na bana, inda kuma ya yi alkawarin yin gyara a kan kura-kuran da aka samu wanda ba za a rasa ba nan da can; tare da bayyana aniyar gwamnati na nada kwamitin gudanarwan hukumar Alhazan nan bada dadewa ba.

Tun farko dai, a jawabin da ya gabatar yayin bikin mika rahoton, Amirul Hajj na bana, Janar Idris Garba mai ritaya, ya bayyana cewa kwamitin ya gano matsaloli da dama, wadanda ke bukatar sauye-sauye game da abinda ya shafi aikin hajjin, ya kuma ce ya mika godiyarsa ga Allah (SWT) kuma ya yi farin-ciki yadda ya ji gwamna ya furta cewar kwanannan za’a kafa kwamitin gudanarwa wanda yin hakan zai taimaka wa hukumar jin dadin Alhazai kwarai da gaske.

Janar Idris ya ce a cikin matsalolin da ke bukatar gyara; a kwai maganar daukan jami’an kula da jin dadin Alhazai na yankunan kananan hukumomi wato (APWOs) wadanda yawancinsu ba su da cikakken ilimin gudanar da aikin kuma da damansu ba ma’aikatan gwamnati bane, wadanda za su iya aiwatar da duk wani abu da hukumar ke gudanarwa ba tare da bata lokaci ba.

Janar Idris Garba ya kuma nemi hukumar kula da jin dadin Alhazai da ta kula wajen ganin an tantance maniyyata yadda ya kamata ba tare an fuskanci wata matsala ba, musamman a kananan hukumomin mulki da ke jihar.

Bugu da kari, shugaban ya bada shawarar cewa gwamnati ta baiwa hukumar karfin dauka da sallaman jami’an kula da mahajjata na kananan hukumomi dan kauce wa irin kura-kuran da aka tafka a baya, ya kuma yaba da kokarin shugaban hukumar na rike Alhaji Idris Abubakar Azozo da daukacin mambobin kwamitin kula da addini na majalisar dokoki ta jihar da kuma sakataren riko na hukumar kula da Alhazai Alh. Umar Makun Lapai.

A nasa jawabin, sakataren riko na hukumar, Alhaji Umar Makun Lapai, ya sake jaddada goyon bayansa ne ga gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello dangane da irin goyon bayan da yake baiwa hukumar wajen ganin ta aiwatar da ayyukanta ba tare da wani tsangwama ba, ya ce tare da taimakonsa aka samu a karo na farko aka sami kwashe alhazan jihar Neja daga filin jirgin sama na Minna kai-tsaye zuwa Madina a kasa mai tsarki wanda ba a taba yin haka ba a tarihin jigilar alhazai a wannan jiha.

 

 

TAURARUWA