Daga Mohammed Mohammed

gov Abubakar-Sani-Bello-577x450

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello

Kungiyar shugabanin kananan hukumomi ta kasa (ALGON), reshen jihar Neja, ta jinjina wa Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, bisa ga tallafin da ya baiwa wasu kananan hukumomin mulki da ke jihar, da ke cikin kanfar kudin da za su yi amfani da su wajen biyan albashin ma’aikata, wanda a halin da ake ciki yanzu, kimanin watani uku kenan; wasu kananan hukumomin ma watanni hudu ba su biya ma’aikatansu hakkokinsu da ya danganci albashi ba.

Shugaban kungiyar, Alhaji Gambo Tanko Kagara,wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar mulki ta Rafi, shi ne ya bayyana hakan a madadin dukkan shugabannin kananan hukumomin da za su ci gajiyar wannan karimci da gwamna ya nuna.

Gambo Tanko ya bayyana jin dadinsa ne yayin wata ganawa ta musamman da ya yi da manema labarai a Minna.

Shugaban ya kuma yaba bisa ga umurnin kai tsaye da gwamnan ya bayar da cewar daga yanzu,  kudin ‘yan fansho ne za a fara biya a farko kafin biyan kowane  irin kudi; wannan matakin in ji shi, abin yabawa ne ba ma ga masu karban fansho kadai ba, har ma ga ma’aikatan kansu.

Da ya karkata bangaren kwadago, Alhaji Gambo Tanko ya yaba wa kungiyar kwadago dangane da gagarumin aikin da suke gudanarwa na tantance ma’aikata a kananan hukumomi, ya kuma shawarci ma’aikatan da su baiwa kwamitin kungiyar kwadago goyon baya ta yadda za su ji dadin gudanar da aikin.

Alhaji Tanko Kagara ya sake jinjina wa gwamnatin Abubakar Sani Bello bisa ga kwazonsa na ganin jihar Neja na kan gaba wajen noman shinkafa tare da irin tallafin da yake baiwa matasa.

0

TAURARUWA