Daga Abubakar Hassan

1 (43)

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bukaci sarakuna da su kasance masu sa ido a kan dukkan abubuwan da ke gudana a yankunansu domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kuma ganin cewa ba a karya doka da oda ba.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a sa’ilin da yake mika sandar girma ga Sarkin Borgu na 17, Barista Muhammad Sani Haliru Dantoro, Kitoro na hudu, a garin New Bussa da ke Karamar Hukumar Borgu na jihar Neja.

Ya ce akwai bukatar Sarakuna su kasance masu kula tare da mayar da hankali kan al’amuran masarautarsu domin a tantance miyagun mutane daga cikin al’umma.

“Ina kira ga masu sarautar gargajiya da su mayar da hankali sosai kan abubuwan da ke gudana a cikin al’umma. Ku kasance masu kula da abubuwan da ke gudana a masarautunku da kuma jiha baki daya. Dole ne ku guji duk wani abu da zai iya bata maku suna,” in ji Gwamnan.

Ya yaba da irin goyon bayan da yake samu daga majalisar Sarakunan jihar, sannan ya bukaci sabon sarkin shi ma ya yi hakan.

Gwamnan ya kuma bukaci sabon sarkin da ya yi amfani da basirarsa wajen ganin cewa masarautar ta ci gaba.

A nasa jawabin, sabon sarkin ya yi alkawarin yin adalci ga daukacin talakawansa,  sannan ya yi kira a garesu da su taimaka masa da shawarwarin da za su ciyar da masarautar gaba.

Sabon sarkin wanda mahaifinsa tsohon sanata ne a jamhuriya ta uku, ya yi kira ga shugabanni da su kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin ci gaba da kuma hadin kan kasar nan baki daya.

Sarkin wanda ya yi tsokaci game da matsalan cikin gida da jam’iyyar APC mai mulki a kasar ke fuskanta ya ce, “ya kamata shugabannin canji su kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su yi aiki tukuru domin samun hadin kan kasa da kuma ci gaban kasa domin tunawa da hidimar da mahaifinsa ya yi.”

Ministan babban birnin tarayya, Abuja,  Alhaji Mohammed Musa Bello da kuma karamin Ministan ma’aikatar Ma’adanai, Honarabul Abu Bawa Bwari ne suka wakilci shugaban kasa, Muhammadu Buhari a wajen bikin mika sandar girman ga sabon Sarkin Borgu.

Bakin da suka sami halartar bikin sun hada da Gwamnan jihar Sakkwato, Honarabul Aminu WaziriTambuwal da Sufeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya, Ibrahim Idris da tsohon Gwamnan jihar na mulkin Soja, Kanar Lawal Gwadabe da kuma Ambasada mai jiran gado, Honarabul Ahmed Musa Ibeto.

Hakazalika,  bikin ya samu halarcin manyan sarakunan kasar nan, daga ciki akwai Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi da kuma Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar.

 

 

 

TAURARUWA