Daga Mohammed Mohammed

assembly

Gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin magance tsaikon da ake samu wajen biyan albashin ma’aikatan jiha.

Wannan matakin da gwamnati ta dauka, ya tilasta wa gwamnati rungumo bashi na sama da naira biliyan biyu a bankin Zenith dake Minna. Tuni dai majalisan dokokin Jihar Neja ta rattaba hannu na amincewa da ciwo bashin.

Bashin da gwamnatin ta rungumo, za ta rinka amfani da shi ne wajen cike gibin da ake samu ta fuskar biyan albashi, sannu a hankali, gwamnatin za ta rika biyan riban kashi 18 na kudin da ta   ranta a karshen kowane wata.

Dan majalisa mai wakiltar Borgu, Hon. Muhammed Abba Bala ne ya hankaltar da ‘yan majalisar dangane da dalilansa a amincewa da rokon da gwamnan ya gabatar a gabansu na su bashi daman ciwo bashin; daga bisani ya samu goyon bayan sauran ‘yan majalisar.

TAURARUWA