Niger state of Nigeria

Gwamnati jihar Neja, ta kafa kwamiti mai mambobi 14 domin su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihar Neja .

Darakta janar na ma’aikatar kula da ala’muran da suka shafi addini, Dokta Umar Farooq Abdullahi ne zai jagoranci kwamitin.

Wasu daga cikin ayyukan kwamintin sun hada da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya tsakanin al’umma. Sauran mambobin kwamitin sun hada da, Alhaji Idris Mohammed dake wakiltan jama’atu Nasril Islam, sai kuma Alhaji Muhammed Liman (Masha-Allah).

Sauran sun hada da Limamin Masallacin Juma’a na Tunga da dai sauran wadanda aka zakulo daga sauran sassa daban-daban. shugaban kwamitin ya bada tabbacin cewar nan ba da jimawa ba ne za’a kafa irin wannan kwamiti wanda zai kunshi mabiya addinin kirista dake cikin jihar. 

TAURARUWA