Daga Mohammed Mohammed

nlc

Gwamnatin Jihar Neja ta kara wa kungiyar kwadago wa’adin watanni uku domin su ci gaba da tantance ma’aikatan da ba su sami zarafin gabatar da kawunansu domin tantance su ba a cikin watanni ukun da suka gabata.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar kwadago na jihar Neja, kwamred Yahaya Idris Ndako a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke kan titin IBB a Minna.

Kwamred Ndako ya ce karin wa’adin ya taso ne kuma ya samu tuburrakkin Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello a lokacin da shugabanin kungiyar kwadago, karkashin shugabancin kwamred Idris Ndako suka kai masa rahoton wucin-gadi da sakamakon tantancenwar da suka gabatar a baya.

Kwamred Ndako ya ce karin wa’adin zai taimaka kwarai wajen tantance wadanda ba su sami halartar tantancewar da aka yi a baya ba, ya kuma bada damar warware wuraren da ake da matsaloli.

TAURARUWA