Mohammed Mohammed

Ma’aikatar ilmi ta jihar Neja na shirye–shiryen gudanar da wassani tsakanin makarantun sakandare da ke fadin jihar Neja.

Wata sanarwa da ta fito daga babban daraktan gudanar da wasanin ma’aikatar, Alhaji Abdulmumini Madami ta ce, wasan zai zo daidai da lokacin da gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello zai cika kwananki dari a karagar mulki.

Alhaji Madami ya ce za’a gayyato daliban daga sashin ilmi 6 da ake das u a fadin jihar inda ma’aikatar za ta canza salo wato za ta rika yin karba-karba a tsakanin sassan.

Daraktan ya yaba wa gwamnatin jihar Neja, da ma’aikatan ilmi bisa ga goyon baya da tallafin kudi da suka basu, domin gudanar da wasani.

Ya ce sakamakon haka sun yi nasarar larshe lambobin yabo sama da 41 a ciki da wajen kasar nan.

Alhaji Abdulmumini ya gode wa iyaye da dalibai da shugabanin makarantu da suke basu goyon baya don

 

TAURARUWA