An dai shirya gasar ne don karrama gwamnan jihar Neja, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu wanda kuma shi ne dan takarar kujerar majalisar dattijai na shiyyar Neja ta kudu a karkashin jam’iyyar PDP.

Kungiyoyin wasan kwallon kafa guda 403 daga kananan hukumomi tara da ke shiyyar ne suka fafata a gasar wanda yana daya daga cikin hanyoyin tabbatar da cewa gwamnan ya samu nasara a zabe mai zuwa da za a yi a wannan mataki.

Kafin wasan na karshe da za a yi a filin wasa na tunawa da Bako Kontagora da ke garin Minna, kananan hukumomin Paiko da ta Gurara suma za su kara don a samu kungiyyar da ta zo ta uku a gasar.

Jagoran gudanar da wasan,

Malam Danjuma Masu, ya ce an samu ci gaba a manufar shirya gasar domin gasar ta baiwa matasa damar sanin muhimman abubuwan da siyasa ke tattare da ita.

Masu ya kuma bayyana cewa wadanda suka yi nasara a gasar wanda aka gudanar a kananan hukumomin guda tara sun samu kyaututtuka wadanda suka hada da kwallaye da kuma rigunan wasanni.

Ya kuma ce kungiyar da ta zo ta daya a gasar baki daya za ta samu kyautar babban kofi, sannan na biya da na uku suma zasu samu kyaututtuka.

Masu ya kuma jinjina wa kungiyoyin wassanin da suka fafata a wasan, sannan ya yi musu godiya da goyon bayan da suka bayar don ganin Gwamna Mu’azu Aliyu ya samu nasara a takarar sa na sanata mai wakiltar shiyyar Neja ta kudu.

A cewarsa, gwamnan mai son cigaban matasa ne kuma idan har aka zabe shi, zai taimaka wajen ci gaban wasannin motsa jiki, a jihar da kuma kasa baki daya, sannan ba da dadewa ba za a sa ranar da za a buga wasan na karshe.

TAURARUWA